ylliX - Online Advertising Network Yan Sanda Sun Cafke Wani Makiyayi Rike Da Tsabar Kudi Miliyan 8.4 Da Makamai A Bauchi - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Yan Sanda Sun Cafke Wani Makiyayi Rike Da Tsabar Kudi Miliyan 8.4 Da Makamai A Bauchi

Yan Sanda Sun Cafke Wani Makiyayi Rike Da Tsabar Kudi Miliyan 8.4 Da Makamai A Bauchi

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani matashin makiyayin shanu dan shekaru 20 mai suna Abubakar Isah da wasu da ake zargi da laifin fashi da makami da garkuwa da mutane da kuma mallakar haramtattun makamai.

A jiya ne aka gabatar da su a hedikwatar rundunar da ke Bauchi Kwamishinan ‘yan sanda Umar Sanda ya ce an kama matashin mai shekaru 20 a ranar 16 ga watan Satumba da tsabar kudi Naira miliyan 8.466,000, bindigar SMG guda daya da tarin manyan harsasai.

An dai kama wayoyi takwas da babur da kuma kwalabe daga hannun wanda ake zargin, kamar yadda ‘yan sanda suka ce Isah ya yi ikirarin cewa ba shi da laifi, ko da yake ya yarda cewa an same shi da duka abubuwan da aka nuna a hannun sa lokacin da aka kama shi.

Isah ya ce shi makiyayi ne da wani Ibrahim yanzu ya ba shi kwangilar kiwon shanu a wani kauye na dan wani lokaci daga nan sai a biya shi.

A ranar da aka kama ni, ina kan kujerar baya na babur wanda shugabana ya hau ya nufi kauyen da zan yi masa kiwon shanu, bai fada min sunan kauyen ba, sai kawai ya tambaya in tafi da shi inji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button