LABARAI/NEWS

yan sanda sun ceto mata tara da za’a yi safarar su zuwa Libya a jihar Katsina

Yan-sanda sun ceto mata tara da za a yi safararsu zuwa Libya a Jihar Katsina

An ceto matan ne a yankin Daura inda ake shirin tafiya da su Nijar kafin a kai su Libya An ceto matan ne a yankin Daura inda ake shirin tafiya da su Nijar kafin a kai su Libya

‘Yan-sanda sun ce sun yi nasarar ceto wasu mata tara da suka fito daga wasu jihohin Najeriya daban-daban da ake shirin safararsu zuwa kasar Libya, a ranar Laraba.

Kakakin rundunar ‘yan-sandan JIhar Katsina, SP Gambo Isah, wanda ya bayyana haka, ya ce sakamakon bayanan sirri da suka samu ne jami’ansu suka yi wa wata maboya ta masu safarar dirar-mikiya a yankin karamar hukumar Daura inda suka ceto matan.

kakakin yan sanda ya yi bayani kan matan inda ya ce wadanda aka ceyo su ne Timilaye Ojo mai shekara 26 daga Jihar Lagos da Blessing Joseph mai shekara 19 daga Jihar Edo da kuma Khadija Abdullahi mai shekara daga Jihar Ondo

Haka kuma akwai Safiyyat Ahmed mai shekara 21 daga Jihar Lagos da Precious Nuhu mai shekara 22 daga Jihar Kaduna da kuma Bolanle Adewusi mai shekara 32 daga Jihar Ogun

Kakakin ya ce Sauran su ne Okpoekwu Eunice mai shekara 28 daga Jihar Enugu da Kabirat Azeez mai shekara 19 daga Jihar Ondo da kuma Taiwo Adeolo mai shekara 27 daga Jihar Ondo

Mai magana da yawun ‘yan-sandan ya ce, a yayin binciken da suka yi sun gano cewa an dauko matan daga Jihar Kano ne zuwa Daura a jihar Katsina, a mota, wadda direban ya gudu ya bar matan bayan da ya ga ‘yan-sanda.

Ya kara da cewa za a kai su kasar Libya ne ta Nijar, kafin a ceto su, tare kuma da bayar da tabbacin cewa za a kamo masu safarar kasancewar ana ci gaba da gudanar da bincike.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button