LABARAI/NEWS

Yan sanda Sun Gargadi ‘Yan Siyasa Kan Amfani Da ‘Yan Daba A Kamfen

Yan sanda Sun Gargadi ‘Yan Siyasa Kan Amfani Da ‘Yan Daba A Kamfen

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta gargadi ‘yan siyasa kan daukar ‘yan daba domin samun kariya a zaben 2023 mai zuwa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Haruna Garba ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da ‘yan sandan suka shirya domin tunkarar zaben 2023.

 

 

Kwamoshinan ‘yan sandan ya ce dokar zabe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima ta amince da ‘yan sanda da hukumomi ‘yan uwanta ne kawai a matsayin wadanda aka ba su damar samar da tsaro a duk lokacin aikin.

Don haka Kwamishinan ya yi gargadin cewa duk wani dan siyasa da aka samu da makami a lokacin zaben za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya.

Garba ya kuma shawarci jam’iyyun siyasa da su guji zage-zage, kalaman kyama da kuma nuna sha’awar rikici Garba ya kuma shawarci jam’iyyun siyasa da su guji zage-zage, kalaman kyama da kuma nuna sha’awar rikici.

A cewarsa, “Babu wani abu mai muhimmanci da ya kai jinin Dan Adam; idan aka kayar da kai, za ka iya yin nasara a nan gaba.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button