LABARAI/NEWS
Yan Sanda Sun Kama Maharan Da Suka Addabi Abuja Da Nasarawa

Yan Sanda Sun Kama Maharan Da Suka Addabi Abuja Da Nasarawa
Rundunar Yan Sandan babban birnin tarayya ta cafke gungun wasu mutum 10 da ake zargin su da kai hare-hare a Abuja da Jihar Nasarawa
Da ake gabatar da su a gaban Kwamishinan Yan Sandan Babban Birnin Tarayya ya ce an kama wadanda ake zargin a wani otel da ke Abuja
An samu bindiga kirar AK-47 sai kwanson harsashi da kuma kananan bindigogi
Ragowar abubuwan da aka samu a wajensu sun hada mota kirar Toyota Camry katin aikin wani dan sanda da kuma janareto guda biyu