ylliX - Online Advertising Network Yan sanda sun kama wasu mutane 2 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Jigawa - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Yan sanda sun kama wasu mutane 2 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Jigawa

Yan sanda sun kama wasu mutane 2 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Jigawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa tare da hadin gwiwar kungiyar ‘yan banga na yankin sun cafke wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a karamar hukumar Taura da ke jihar

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Lawan Shiisu, ya tabbatar da kamen a wata hira da manema labarai a Dutse

Shiisu ya ce wanda ake zargin mai shekaru tsakanin 35 zuwa 40, an kama shi ne a ranar Lahadin da ta gabata sakamakon ingantattun bayanan sirri da kuma sahihan bayanai

Wadanda aka kama ana kyautata zaton ‘yan kungiyar masu aikata laifuka ne da suka addabi sassan jihar da kuma makwabtan Kano

Yan sanda sun kama su ne a wani samame na musamman a kauyen Larabawa da ke yankin Gabasawa a Kano da kuma kauyen Larabar Gurgunya da ke Taura a Jigawa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button