ylliX - Online Advertising Network Yan sanda uku sun mutu sakamakon hatsarin motar dakon kuɗi a Jihar Kebbi - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Yan sanda uku sun mutu sakamakon hatsarin motar dakon kuɗi a Jihar Kebbi

‘Yan sanda uku sun mutu sakamakon hatsarin motar dakon kuɗi a Jihar Kebbi

‘Yan sanda uku da fararen hula uku sun ƙone ƙurmus sakamakon hatsarin da motar dakon kuɗi ta bankin Eco ta yi a garin Argungu na Jihar Kebbi.

Cikin wata sanarwa, kakakin ‘yan sandan Kebbi, Nafiu Abubakar, ya ce wasu mutum biyar sun ji raunuka, uku daga ciki ‘yan sanda, lokacin da motar ta yi karo da wasu ababen hawa huɗu a kan Titin Argungu zuwa Birnin Kebbi ranar Talata.

Lamarin ya faru ne lokacin da mota ƙirar Carina E da ke ɗauke da jarkokin man fetur ke gudu saboda jami’an hukumar Kwastam na biye da ita daga Birnin Kebbi a cewar sanarwar Bayan ta isa ƙauyen Jeda, sai motar ta yi karo da motar dakon kuɗin kuma ta kama da wuta tare da ƙone wasu motocin uku.

Motoci biyar ne da kuma babur ɗaya suka ƙone a gobarar da kuma mutum shida da suka mutu, ciki har da ‘yan sanda uku Kazalika, mutum biyar uku daga ciki ‘yan sanda sun ji raunuka kuma an kai su asibitin Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kebbi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button