LABARAI/NEWS
Yan Sandan Jahar Katsina Sun Cafke Wani Mai Garkuwa Da Mutane Da sace Shanu

Yan Sandan Jahar Katsina Sun Cafke Wani Mai Garkuwa Da Mutane Da sace Shanu
Rundunar yan sandan jahar Katsina ta cafke wani kasurgumin dan bindiga mai suna Adamu Abdulraham mai shekaru 30 mazaunin kauyen Cidawaki a karamar hukumar Safana ta jahar.
Ana zargin matashin da kaiwa al’umomin Safana harehare da garukuwa da mutane da kuma satar shanun jama’a
Kakakin rumdunar yan sandan jahar Kataina ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa da cewar yana daga cikin yaran wani mai suna Lawan Dantarugu da yanzu haka ya buya a daji
Binciken farko farko da jami’an yan sanda suka gabatar akan sa ya ce sun sha kai harehare Safana da kuma Dutsinma tare yin garkuwa da mutane da kore mu su shanu