LABARAI/NEWS

yan sandan jihar Gombe sun kama wasu mutum 23 da laifin tada zaune tsaye

Rundunar yan sandan jihar Gombe ta kama wasu mutum 23 da laifin tada zaune tsaye a yankin Malan-Inna quarters

Matasan wadanda akewa lakabi da ‘Yan Kalare sun shahara wajen aikata muggan laifuka a wasu sassan jihar Gombe

Yayin holin masu laifin a shalkwatar rundunar dake Gombe, an kama matasan dauke da muggan makamai da suka hada da adda 15 gatari 1 da sauran su

Haka zalika rundunar ta kama wani matashi mai suna Mustapha Adam Usman dan asalin jihar Kano dai laifin zamba cikin aminci

Wannan matashi ya je shagon cirar kudi na POS da niyyar sa kudi a wani asusun banki kimanin naira dubu 50, wanda kuma bayan sa kudin ne ya bawa mai shagon kudin jabu ba tare da ya sani ba

A cewar mai shagon mai suna Mannir Mohammed, sai bayan da ya tafi ne yaga wadannan kudi sun zama takaddu Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ASP Mahid Mu’azu yace ana cigaba da bincike, kuma da zarar an kammla za’a gurfanar da mai laifin

Kwamishinan yan sandan jihar Gombe Ishola Babaita ya gargadi iyayen yara da su kasance suna sa ido akan zirga zirgar yaransu domin gujewa tarayya da masu laifi Sannan ya bukaci sanar da jami’an rundunar duk wani motsi da ba’a gamsu da shi ba

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button