LABARAI/NEWS

‘Yan siyasa sun tunzura ni fitowa takara, sai da su ka tatse ni sannan su ka tsere, Tsohon IGP

‘Yan siyasa sun tunzura ni fitowa takara, sai da su ka tatse ni sannan su ka tsere, Tsohon IGP

Tsohon sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Mike Okiro, ya bayyana yadda wasu ‘yan siyasa su ka dinga yi masa angiza mai kantu ruwa, ya cire makudan kudade don tsayawa takarar sanata bayan ya yi murabus, Daily Trust ta ruwaito.

Okiro ya yi wannan bayanin ne a Abuja, yayin wani taro mai taken: “Hanyar tattaunawa da ‘Yan takarar Shugaban Kasa”, wacce New Nigeria Dream Initiative (NNDI) ta shirya inda ya ce wasu mutane ne su ka hada masa tarko har su ka sanya shi shiga siyasa bayan ya yi murabus wanda a hankali su ka tatse kudadensa ya kare babu ko sisi.

Ya koka akan yadda ‘yan Najeriya a kullum su ke da burin amsar kudi don zaben dan siyasa, inda ya ce wannan ne babbar matsalar gwamnati.

A cewarsa:

“Yan Najeriya su na yawan kuka da shugabanci, amma na kan ce ba haka bane. Idan an samu shugaba na kwarai, ya kamata a samu mabiya na kwarai. Saboda idan shugabanni su na shirmensu mu na dariya ne mu na daga musu hannu su ma su dago mana hannu.

Amma ba daidai ba ne. Su na sauyawa, su na bayar da kudi don a zabe su. Ku na amsar kudi don zaben mutum ko da bai cancanta ba. Sai su ba mutum N5,000 don ya zabe su, ya ci gaba da fama tsawon shekaru 4. Kenan N5,000 ce za ta ishi mutum rayuwar shekaru 4.
“Na yi takarar sanata a Abuja. Lokacin da aka nemi in yi takara ban dade da murabus ba. Na ce to amma zan yi shawara. Da na nemi shawarar matata cewa ta yi tsoro ta ke ji.
“Haka su ka dinga bibiyata, in kawo kudi za su yi wancan, za su yi wannan. A haka sai da na karar da duk kudina har ta kai ga ban da ko sisi. Su ka dinga yaudarata.
“Ubangiji ya taimakeni ma ban yi rancen kudi ba, da na kwana ciki.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button