LABARAI/NEWS

Yan Ta’adda Sun Kai Mamaya Kan Al’ummar Zamfara, Sun Sace Basaraken Gargajiya, Da Dan’uwan sa

Yan Ta’adda Sun Kai Mamaya Kan Al’ummar Zamfara, Sun Sace Basaraken Gargajiya, Da Dan’uwa

Yan ta’adda sun yi garkuwa da Hakimin Birnin Tsaba a karamar hukumar Zurmi a Jihar Zamfara.

Wanda aka dauke mai suna Alhaji Hashimu, an dauko shi ne tare da kanensa mai suna Danbalange wanda dan jam’iyyar All Progressives Congress ne a yankin.

Wani dan yankin, Mohammed Faruku, ya ce an yi garkuwa da hakimin gundumar da dan uwansa a gidajensu da misalin karfe 4:30 na safiyar ranar Juma’a.

Faruku ya ce yan ta’adda da ke kan babura sun kama mutanen biyu daga gidajensu a Birnin Tsaba.

Wani dangin wadanda abin ya shafa da ya nemi a sakaya sunansa saboda fargabar harin, ya shaida wa Daily Trust cewa Wani dan ta’adda ne ya kaddamar da harin a kan mutanen biyu. Ya kira mu ta waya ya tabbatar da sace mutanen da ‘yan kungiyarsa suka yi

Ya kara da cewa an yi garkuwa da mutanen ne sakamakon kwace sabbin babura guda biyu mallakin shugaban ‘yan ta’addan da jami’an tsaro suka yi

Dan gidan ya ce Sarkin ‘yan ta’addan ya kuma yi barazanar cewa tun da gwamnati na sane da babura da jami’an tsaro suka kwace, wadanda abin ya shafa za su fuskanci fushinsa.

Wani dan uwa na mutanen biyu, Idris Abdullahi, ya ce, “Muna bakin kokarinmu don ganin an sako su cikin gaggawa. Mun fara tattaunawa da sarki.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Shehu, an kasa samunsa ta wayar tarho domin jin ta bakinsa har zuwa lokacin hada wannan rahoto

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button