ylliX - Online Advertising Network Yan Ta’adda Sun Kai Wa Sojoji Nigeria Harin Kwantar Bauna A Babban Birnin Abuja gidan yarin kuje - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Yan Ta’adda Sun Kai Wa Sojoji Nigeria Harin Kwantar Bauna A Babban Birnin Abuja gidan yarin kuje

Yan Ta’adda Sun Kai Wa Sojoji Nigeria Harin Kwantar Bauna A Babban Birnin Abuja gidan yarin kuje

Yan ta’adda sun farmaki wasu sojoji da ke sintiri a kan hanyar Kubwa zuwa Bwari da ke birnin tarayya Abuja
Wasu rahotannin sirri sun bayyana cewar ‘yan ta’addan na shirin kai hari makarantar koyon aikin lauya da ke Bwari da wasu cibiyoyin gwamnati a Abuja

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce harin na nuni da cewa ‘yan ta’addan sun mamaye birnin tarayya amma hukumomi sun ce suna kokarin gano maharan

A cewar daya daga cikin majiyoyin, wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun yi wa dakarun sojin da ke sintir a kan hanyar Kubwa zuwa Bwari kwanton bauna

Ya kara da cewa sojoji uku daga cikin dakarun sun jikkata yayin harin kuma an kwashe su zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu

Harin da aka kai a yankin na Bwari ya nuna cewa a zahiri ‘yan ta’addan suna nan a wurin kuma akwai yiwuwa su kai farmaki makarantar koyon aikin lauya da ke Bwari kamar yadda aka bayyana

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button