Girki Adon Uwargida

YANDA AKE YIN MADARAR WAKEN SOYA.

YANDA AKE YIN MADARAR WAKEN SOYA.

Idan kuka karanta ku turawa sauran yan uwa domin su amfana.

Mataki Na – 1

Za a fitar da duk wani datti da aka san yana jikin Waken Soya din, a kuma tabbatar babu dattin a ciki duk an kautar da shi.

Mataki Na – 2

Za a sanya ruwa a kan Wuta ya tafasa, idan y kammala tafasa sai a dauko Waken Soyan nan da aka gama tsincewa a zuba a cikin wannan ruwan zafin, sai a dunga juyawa da Cokalin miya har sai ya dibi kimanin mintuna 10 haka. Sannn sai a sauke.

Mataki Na – 3

Idan an sauke, za a zuba a cikin Kwandon tace Shinkafa. Kunga kenan ruwan zafin da yake ciki zai tsiyaye a kasa, to sai a dauko ruwan sanyi a yayyafa akan Waken Soyan, Amma ruwan sanyin kadan-kadan fa. Domin hakan zai taimaka Bawon jikin Waken Soyan ya tattaso sama tunda ya jiku.

Mataki Na – 4.

Sai a saka hannu duk biyun a dunga murje Waken na yanda duk za a fitar da bawon jikin Waken Soyan. Kamar dai yanda ake yiwa Waken yin Alala, ko kuma Kosai. Idan an kammala fitar da Bawan sai a wanke Waken Soyan sosai da sosai.

Mataki Na – 5

Za a dora ruwa a kan Wuta a karo na biyu kenan, sannan sai a bar ruwan ya tafasa, idan anga ya tafasa, sai a dauko wannan Waken Soyan da aka kammala wankewa sai a zuba a cikin tafashash-shen ruwan, sannan sai a dunga juyawa har zuwa lokacin da za a ga Waken ya dahu. Yana iya daukan mintuna 25 ko fiye da haka kafin ya dahon. ( A lura. Ruwan da za a dunga zuba Waken a ciki dole ya dunga zama wadatacce ne yanda bazai yiwa Waken kadan ba

Mataki Na – 6.

Idan an kammala dafa Waken Soyan, sai a sauke, sannan a tace ruwan, za a ga Waken Soyan duk ya babbare bibbiyu, kamar dai gyada a barata biyu hakan zai zama. To sai a barshi duk ruwan ya gama tsanewa gaba daya.

Mataki Na – 7

A wannan Matakin dole a lura sosai domin shine matakin da ake bi wajen busar da wannan Waken Soyan da aka kammala dafawa yanzu.

*- Za a iyi busarwa da zafin rana

*- Za a iya busarwa da zafin Oven

*- Za a iya busarwa da prawn

*- Za a iya busarwa da duk wata hanya da aka san idan an busar dashi zai bushe sosai da sosai.

Mataki Na – 8

Idan ya gama bushewa, sai a dauko shi a zuba a cikin Blendar a nika sosai da sosai. A tabbatar nikan yayi laushe sosai fa. Idan an gama nikawa sai a dauko abin tankadewa mai laushi sai a tankade yanda zayyi laushi da gaske.

Za a sami mazubi mai murfi sai a zuba a ciki a kuma rufe. Za a iya daukan watanni uku kuna amfani da kayan ku kadan-kadan.

Ku yi like, da kuma sharing dan yan uwa na waje su amfana

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button