ylliX - Online Advertising Network YANZU YANZU A kai kasuwa Kamfanin BUA ga Gwamnatin Kogi - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

YANZU YANZU A kai kasuwa Kamfanin BUA ga Gwamnatin Kogi

YANZU-YANZU: A kai kasuwa_Kamfanin BUA ga Gwamnatin Kogi.

Kamfanin BUA ya mayar da martani ga Gwamnatin Jihar Kogi akan batun wani fili mai girman kadada dubu 50 da ake zarginsa da mallaka ba tare da biyan sisin kobo ba.

A wata wasiƙa da ya turawa Jihar Kogi a yammacin yau Talata, Kamfanin yace shi fa baya bukatar wannan fili da ake taƙaddama a kansa.

A cewar Kamfanin, tunda farko dama Gwamnatin Jihar Kogi ce ta nemi da a bashi wannan fili domin ya yi amfani da shi wajan samar da masana’antu a Jihar, amman saboda wasu dalilai guda 3 Kamfanin ya gaza samar da waɗannan masana’antun.

Dalilan da Kamfanin ya ayyana a wasiƙar sun haɗa da rashin cika alƙawarin da gwamnatin Jihar ta yi na samar da titin da zai bada dama a sami hanyar zuwa filin domin fara yin aikin samar da masana’antun, rashin tsaro a yankin da filin yake sai kuma sakamakon bincike da ya nuna cewa ƙasar filin ba za ta bada dama Kamfanin ya samar da waɗannan masana’antun da ya kudiri niyya ba.

Don haka a ƙarshe Kamfanin na BUA ya nuna rashin buƙatarsa ga wannan fili, inda yace wa Gwamnatin ta Kogi a kai kasuwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button