ylliX - Online Advertising Network YANZU-YANZU: APC ta rubutawa INEC cewa ta amince da Ahmad Lawan a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Yobe ta Arewa - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

YANZU-YANZU: APC ta rubutawa INEC cewa ta amince da Ahmad Lawan a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Yobe ta Arewa

YANZU-YANZU: APC ta rubutawa INEC cewa ta amince da Ahmad Lawan a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Yobe ta Arewa

Jam’iyyar All Progressives Congress ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, da ta amince da Ahmad Lawan a matsayin dan takararta na Sanata a Yobe ta Arewa a 2023, in ji Peoples Gazette.

A wata wasika da ta aike wa INEC ranar 14 ga watan Yuni, 2023, jam’iyyar APC ta bayyana aniyar ta na dora sunan Mista Lawan a matsayin dan takararta na satana a Yobe ta Arewa, duk da cewar ta kira Bashir Machina a matsayin wanda ya lashe tikitin aprimary watan da ya gabata.

Mista Machina ya dage cewa ba zai mika wa Lawan wa’adin sa ba saboda ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani na sanata ne a lokacin da shugaban majalisar ya je Abuja yana neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki.

Mista Lawan ya rasa tikitin ne a hannun Bola Tinubu a ranar 8 ga watan Yuni kuma ya koma gundumarsa inda ya nemi tikitin jam’iyyarsa ta tsayawa takarar Sanata a karo na shida.

Mai magana da yawun hukumar ta INEC bai mayar da wata bukata ta neman yin tsokaci kan ko ofishin zaben ya gamsu da bayanin da jam’iyya mai mulki ta yi na mika sunan Mista Lawan ko a’a.

Wani mai sharhi kan harkokin shari’a Chioma Okechukwu ya ce matakin da jam’iyyar APC ta dauka bai dace ba, kuma Mista Machina zai samu dama mai kyau a kotu.

Ms Okechukwu ta ce “Suna bukatar izininsa don maye gurbin sunansa tun da ya ci zaben fidda gwani a bisa doka.”

“Jam’iyyun siyasa na da hurumin tantance ‘yan takara, amma kuma dole ne INEC ta yi iya bakin kokarinta don ganin cewa kowane dan takara ya bi ka’idojin da doka ta tanada.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button