ylliX - Online Advertising Network Yanzu Yanzu || Buhari ya tsige shugaban Hukumar NYSC Birgediya M Fadah - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Yanzu Yanzu || Buhari ya tsige shugaban Hukumar NYSC Birgediya M Fadah

Yanzu Yanzu || Buhari ya tsige shugaban Hukumar NYSC Birgediya M Fadah

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya tsige shugaban hukumar yi wa matasa hidima na kasa, Birgediya Janar Mohammed Fadah.

Da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar NYSC, Eddy Megwa, kawai ya bukaci wakilinmu da ya jira wata sanarwa a hukumance da za a fitar ranar Juma’a.

 

 

Sai dai jaridar The Cable, ta nakalto majiyoyin na cewa shugaban ya dauki matakin ne a ranar Alhamis.

Korar Fadah na zuwa ne watanni shida kacal bayan nada shi shugaban NYSC a watan Mayu, 2022.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button