YANZU-YANZU: Musulmi za su yi azumi har sau biyu a shekarar 2030

YANZU-YANZU: Musulmi za su yi azumi har sau biyu a shekarar 2030
Masu ilmin taurari sun ce a shekarar 2030 mai zuwa, Musulmin duniya za su yi azumin watan Ramadan har sau biyu.
Azumi na farko a watan Janairu, na biyu kuma a karshen watan Disambar shekarar, yanayin da tun 1997 ba a taba gamuwa da shi ba.
BBC ta ruwaito Babban dalilin aukuwar haka shi ne bambancin da ke tsakanin shekarar Musulunci da ake lissaftawa da bayyanar wata, da kuma shekarar nasara wadda aka danganta da kwanakin da duniya ke dauka kafin ta zagaya rana.
Sannan wannan yanayin a aukuwa ne sau daya cikin shekara 30 saboda shekarar Hijira ba ta kai tsawon ta nasara da kwanaki 11 ba, kamar yadda Khaled al-Zaqaq, wani mai nazarin taurari dan kasar Saudiyya ya bayyana a Twitter.
Tsawon shekara guda ta Hijira kwana 354 ne, inda shekarar nasara kuwa ke da kwana 365.
Rahoton BBC Hausa