LABARAI/NEWS

Yau naga abun mamakin da ban taba gani ba a wurin Sallar dare (Tahajjud) yadda ‘yan mata suka cika makil

Yau naga abun mamakin da ban taba gani ba a wurin Sallar dare (Tahajjud) yadda ‘yan mata suka cika makil

A tsawon shekarun da nayi ina halartar sallar Tahajjud, ban taba ganin lokacin da ‘yan mata suke cika masallaci kamar wannan lokacin ba.

Tabbas nayi matukar mamaki da ganin hakan saboda a masallacin da nayi Sallah, zan iya cewa zai yi wahala mazan sufi mata yawa.

Me Yasa ‘Yan Mata Suke Cin-ci-rindo Domin Halartar Sallar Tahajjud?

Idan muka yi duba da yanayin zaman lafiya da kwanciyar Hankalin da muke ciki a jihar mu ta Gombe a wannan lokacin, zamu iya cewa bamu san wani abu da ake cewa rashin tsaro ba, idan muka kwatanta da wasu daga cikin jihohin da suke fama da matsalolin rashin tsaro.

Zaman lafiyan da muke ciki ya bawa ‘yan mata damar fitowa hankalinsu kwance, kuma yawanci ‘yan matan da iyayen su Mata suke zuwa, wasu kuma da ‘yan uwansu amma da wahala kaga budurwa ita kadai tazo saboda an musu tsari mai kyau a masallatai da dama na cikin kwaryar jihar Gombe.

Abu na karshe da nike ganin ya sabba zuwan ‘yan mata da dama shine; a wannan zamanin da muke ciki tabbas mazajen Aure sunyi karanci, amma ba zaka gane hakan ba, sai lokacin da kake son ka aurar da ‘yarka ko ‘yar uwarka zaka fahimci hakan.

Mata da dama suna son Aure amma samun tsayayyen saurayin da zai Aure su shine tashin hankalin, bance ba’a yin Aure ba, duk wanda yake jihar Gombe yasan irin yadda ake yawaita yin Aure a kowane mako kafun shigowar watan Ramadan.

Duk da Auran da ake yi a jihar, kamar ba ‘yan matan garin ake Aura ba, saboda yadda ‘yan matan suka yi yawa a cikin garin.

Dole tasa hakan ‘yan mata da dama suka dukufa ka’in da na’in suna ta rokon Ubangiji Allah ya basu mazajen Aure, wasu kamma ance har sunan saurayin da su so, suke ambata a cikin sujjada. Kaga kuwa duk wanda wata budurwa ta ambaci sunanshi to da alama zai angonce bayan Sallah ko da kuwa bai shirya ba matukar Ubangi ta amshi Addu’arta.

Ina yiwa dukkannin samarin da suke son Aure fatan samun matan Aure na gari, suma matan

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button