LABARAI/NEWS

yau ne wata babbar kotun jihar Kano ta ci gaba da sauraren shari’ar ɗan chaina

Yau ne wata babbar kotun jahar Kano ta ci gaba da sauran shari’ar ɗan ƙasar Chaina mai suna Geng Quanrong da ake zargi da yin amfani da wata wuƙa ya Hallaka Ummulkursum Sani Buhari

A zaman kotun na yau Alhamis an karanto wa Dan china ƙunshin tuhumar da ake yi masa nan ta ke ya musanta zargin da ake yi masa.

Daman tun a zaman Kotun baya lauyan wanda ake zargin ya roƙi kotun da samar masa da mai yi masa fassara daga harshen turanci zuwa harshen Mandarin na ƙasar Chaina.

Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji ya bayar da umarni ga ofishin jakadanci Sin a Nijeriya da ya turo da wanda zai dinga yi masa fassara kamar yadda tsarin dokokin Shari’a yake.

A wannan rana dai ofishin jakadanci Sin ya turo Wani mai suna Mista Guo Cumru amatsayin Wanda yayi masa fassara

A na zargin Geng Frank Quarong da aikata laifin kisan kai wanda ya saba da sashi na 221 ƙaramin sashi na 2 na dokokin shari’a na jahar Kano 2019 wanda ya musanta zargin.

Lauyan gwamnatin jihar Kano Barista Musa Abdullahi Lawan, ya bayyana cewa daman shi wanda ake tuhuma ya ce” dole sai an zo masa da mai fassara daga harshen turanci zuwa Chanis.

Shima barrister Abdullahi Yusuf Adamu ɗaya daga cikin lauyoyin wana ake tuhuma yayi koke Game da wasu sabbin fuskoki da yace ya Gani Suna sa’ido Gane da shari’ar

“A cewarsa shirye suke su kawo shaidun su domin mu sani cewa sun san abinda ya faru ko basu sani ba.

Kuma abun da aka yi shi ne adalci domin kundin tsarin mulkin ƙasa ya ce ” duk wanda ake tuhumar sa da laifi wanda ake amfani da harshen da bai sani ba dole ne kotu ta samar masa da wanda zai fassara masa daga wannan Yaren zuwa Yaren da yake ji wannan shi ne ƙa’idar dokokin mulkin ƙasa.

Sai dai anasa bangaren barista Abdullahi Adamu ya ce sun yi suka akan shigowar wasu lauyoyi a matsayin masu sanya ido a wannan Shari’ar , da yace a tsarin shari’a wannan wani sabon abu ne ,wanda anan gaba za mu yi tsokaci akai na bayyanar wasu lauyoyi.

Lauyan ya yi zargin akwai wata maƙarƙashiya da ake shirin saka wa a cikin shari’ar.

” Babu wani abu da ake kawo wa ake masu sanya ido in ba a ƙaƙanan kotuna ba, domin sai a Shari’a ta neman kuɗi ita ce kawai za a iya yin wannan abu.

Tuni dai Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji ya saka ranakun 16, 17 18 ga watan Nuwamba 2022 domin fara gabatar da shaidu a gaban kotun.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button