ylliX - Online Advertising Network Yawaitar Hare-haren 'Yan Bindiga Ya Kashe Mutum 465, A Cikin Wata Guda A Najeriya - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Yawaitar Hare-haren ‘Yan Bindiga Ya Kashe Mutum 465, A Cikin Wata Guda A Najeriya

Yawaitar Hare-haren ‘Yan Bindiga Ya Kashe Mutum 465, A Cikin Wata Guda A Najeriya

Daya daga cikin kungiyoyin farar hular da ke bibiyar lamurrar harkokin tsaro a Najeriya mai suna Connected Development ta ce akalla mutane 465 yan ta’adda suka kashe tare da yin garkuwa da wasu mutane 355, a fadin kasar cikin watan yunin da ya gabata

Yayin gabatar da rahoton da aka wallafa jiya Laraba a birnin Abuja fadar gwamnatin Najeriya babban jami’in bincike da tsare tsare na kungiyar farar hular ta Connected Development Ani Nwachukwu ya ce baya ga dimbin rayukan da suka salwanta mutum dubu 2,000 akasarinsu daga yankunan karkara sun rasa matsugunansu, yayin da wasu 120 suka samu raunuka daban-daban a hare-haren da suka rutsa da su

Rahoton ya kuma koka kan yadda acikin shekarun da suka gabata gwamnatin Najeriya ta kara yawan kudaden da ake kashewa don karfafa sojojinta da sauran ayyukan inganta harkokin tsaro a kasar amma duk da haka ba a samu saukin hare-haren yan ta’adda yadda ake sa rai ba

A cikin watan Yulin da ya gabata ne dai wani bincike da jaridar Premium Times a Najeriya ta yi ya bayyana cewar yan ta’addan sun kashe jami’an yan sanda akalla 65, da sojoji 81, da jami’an NDLEA biyu sai kuma jami’an Civil Defence 5, da kuma ma’aikatan hukumar kiyaye hadurra ta FRSC 2 daga watan janairu zuwa Yunin shekarar da muke ciki

Sakamakon binciken da aka tattara daga rahotannin kafafen yada labarai ya nuna cewa an samu asarar dubban rayuka a rabin farkon shekarar 2022, inda kimanin mutum 3,000 suka mutu acikin watanni uku na farkon shekarar ciki har da jimillar jami’an tsaro 157 da yan ta’adda suka kashe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button