LABARAI/NEWS

ZA A SAUYA FASALIN WASU DAGA CIKIN KUDADEN NIJERIYA

ZA A SAUYA FASALIN WASU DAGA CIKIN KUDADEN NIJERIYA

A kokarin ta na rage matsin tattalin arzikin da ake ciki da kuma samun damar rarraba kudade a Nijeriya, Babban Bankin kasa wato (CBN) yace zai sauya fuskar wasu kudade a cikin kasar nan.

Babban bankin yace ‘yan Nijeriya nada kwanaki 37 talatin da nakwai kacal don sauya tsaffin kudaden su zuwa sababbi.

Sabbin kudaden da suka hada da naira dari biyu ( N200), Naira dari biyar (N500), da Naira Dubu daya (1000) Za su fara Zagayawa cikin Qasar nan daga 15, Ga Watan Disamba, 2022.

Inda Su kuwa Tsaffin Kudin da ake Anfani da su za a daina karbar su Daga 21 ga watan Janairun 2023 cewar Shugaban babban bankin na kasa Mista Godwin Emefiele.

Bayan nan shugaban Babban bankin yace Mutanen da suke da kudade a hannun su za su fara Iya zuba su a cikin asusun bankin su daga ranar alhamis 27 ga watan Octoba 2022, Inda babu wanda zai cajesu sisin Kobo kafin fara raba sabbin kudaden, Inda suke da kwana dari 100 don sauya tsaffin kudin su zuwa Sababbi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button