ylliX - Online Advertising Network Za a yi bincike kan zargin cin zarafin ƴar sanda a Osun - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Za a yi bincike kan zargin cin zarafin ƴar sanda a Osun

Za a yi bincike kan zargin cin zarafin ƴar sanda a Osun

 

Sifeta-janar na ƴan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya bayar da umurnin a yi bincike kan zargin wani ɗan sanda da cin zarafin wata jami’ar ƴan sanda a jihar Osun, da ke kudu maso yammacin ƙasar.

A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, wata ƴar sanda mai suna Olorunsogo Bamidele ta yi zargin cewa wani abokin aikinta ɗan sanda ya ci zarafin ta kuma ya yi barazanar harbin ta saboda ta ƙi yarda da tayin da ya yi mata na soyayya.

 

 

A cikin bidiyon, Olorunsogo, wadda matar aure ce ta nuna raunukan da ta samu sanadiyyar cin zarafin nata, ta kuma zargi abokin aikin nata da ƙoƙarin ɓata mata suna.

Ta ce “bayan ya buge ni, ya shiga ciki ya ɗauko bindiga inda ya yi barazanar harbi na. Amma sai wasu mutane suka fitar da ni daga ofishin suka ce min na gudu, amma na ce ba zan gudu ba, ya kashe ni.”

Bidiyon dai ya janyo martani daga al’ummar Najeriya a shafukan sada zumunta.

A wani saƙo da aka wallafa ta shafin rundunar ƴan sandan Najeriya, shugaban rundunar ya ce za a ɗauki matakin da ya dace da zarar sakamakon binciken ya kammala.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button