LABARAI/NEWS

Za’ai tabare kowa ya rasa – Tinubu ya gargadi APC

Za’ai tabare kowa ya rasa – Tinubu ya gargadi APC

Jagoran jam’iyyar APC na kasa Bola Ahmad Tinubu, ya ce ba wanda zai janyewa cikar burinsa na zama Shugaban kasa, ya kuma yi gargadin cewar matukar ba’a zabe shi a dan takara ba gwara kowa ya rasa.

Shugaban kasa Muhammad Buhari, wanda a yanzu haka yake birnin Spain yace, “Jam’iyyar APC ba zatai zaben fidda gwani ba, za’a fitar da dan takara ne ta hanyar masalaha kamar yadda akai a lokacin samar da sabon shugaban Jam’iyyar a matakin kasa”.

A zaman yau da akai wanda Buhari ya jagoranta da gwamnonin APC kafin ya tafi kasar Spain, an ruwaito cewar, An watse baranbaran tsakanin gwamnonin jam’iyyar APC kan wanda zai yi takarar shugaban kasa a 2023, inda gwamnonin Arewa suka ce dan takarar shugaban kasa daga yankin Kudu ba zai iya kada Atiku Abubakar ba, a don haka dole sai dai a bwa dan ƴankin Arewa takara.

A hannu guda kuma suma gwamnonin yankin Kudu sun ce ba su yarda ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button