FadakarwaIslamic Chemist

ZAFIN JIMA’I [PAINFUL INTERCOURSE]

ZAFIN JIMA’I [PAINFUL INTERCOURSE]

Jin zafi yayin jima’i abune da Mata suka fi korafi kansa, wanda kan faru farko-farko kafin soma penetrating, ko yayin penetrating ko bayan jima’in ya kammala. Ababe daban-daban kan jawo hakan wanda duk akan iya magancesu. Zafin na zuwa ne wani kamar yankan wuka wato sharp, Wasu kuma tunda daga shigar maigida jikinsu har agama.

::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

DALILAN JIN ZAFI A FARKO- FARKON SHIGA

Wato fara jin zafi ga Mace tun kafin kaciyar Namiji ta gama nutsewa a farji sosai ballantana yakai ga deep penetrating amma tuni ta fara jin azaba.

Abunda kan jawo irin wannan zafin ya haɗa da;

■- Toshewar kan wani glands me suna (Bartholin) dake bakin farji gefe da gefe… Wanda shine ke fidda ruwa me yauki, yai lubricating farji yakesa Mace ta rika jinta wet koda ba yayin jima’i ba, musamman in anfarko bacci da asuba, ko doguwar tafiyar kasa da cinyoyi suka rika kaikomo… ballantana kuma yayin motsawar sha’awa.

Wanda wannan ne Mata kan canza masa suna suke kiransa ni’ima. Yana toshewa obstruction wani lokacin ma har yadan ja ruwa ana iya gani aji zafin…wani bun saide ya toshe baya jan ruwa.

Toh wani bun in akai wasa da mace kofar kan dan bude asami lubrication amma ba sosai ba, shine sai Mata su rika jin kamar basu da ni’ima… Amma fa ta ciki akwai ruwan lubricans din kurum kofar fitowarsa ce atoshe. Karshe Mace taita zirarar da kudinta abanza wajen shan Maganin Mata.

Shiyasa ko addini aka shawarci a fara da wasanni wato foreplay kafin fara saduwa inba wannan jima’in na iya komawa azaba baki daya musamman ga Macen maimakon jin dadi.

■- Saukar ko raguwar sinadarin estirojen ajika ga Macen da ke dab da daina haila wato shekara 45 zuwa sama, koma wacce ta dena haila din saboda bushewar da gaban keyi (atrophic changes of vagina),
Ko wacce tana haila amma kuma ta jima bata haihu ba koma ta dena don harta manta dawainiyar goyon ciki, Ko kuma ga Macen dake shayarwa itama na iya fuskantar hakan.

■- Ko kuma sakamakon nau’in wasu magunguna da Mace ke sha dakan kai ga dauke damshi a farjin Mace wanda hakan kansa jin zafin: Magunguna irin na hawan jini, Magungunan sa bacci, Magungunan farfadiya (seizure), Magungunan kawar da damuwa (anti depressant), dana borin jini, Mura, dana bada tazarar haihuwa.

■- Jin rauni a farji sakamakon ƙuna da ruwan zafi, rauni ta hanyar sanya yatsa cikin farji ya zamto farcen mutum ya haifar da raunin, ko tura wani abun daban kamar Dildos, ko sakamakon aiki akugun Mace dalilin karaya [Pelvic fructure].

■- Sakamakon kaciyar Mata da akanyi nanma ga Macen da akama irin wannan wasu kan fuskanci zafin, ko
Sakamakon ƙari da ɗinkin da akan yiwa Mata yayin haihuwa in yaro ya kakare,

■- Ko sakamakon shigar kwayoyin cuta fata da sauran nau’ikan cuttukan fata daka iya shafar farji.

■- Ko Macen dake da matsalar tsukewar farji da ko ýatsa baya shiga [vaginismus] musamman Macen da bata taɓa sanin namiji ba, dama a Amare ake ganin hakan, kwata-kwata gaban namijin baya shiga, ita kanta Macen ture mijin take saboda zafi. Wannan ba abun so bane kamar yadda Matan kanyi kuskuren daukar haka abun tutiya domin karshe basa dandana dadin jima’i saida dauki likita galibi.

:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

SAI KUMA DALILAN JIN ZAFI BAYAN NAMIJI YA GAMA SHIGA CIKI

Wato zafi yayin deep penetration wanda wannan mafi yawa kan faru ne sakamakon wasu cuttuka kamar;

1- Cuttukan Mara, bakin mahaifa
2- Ƙarin cikin mahaifa [fibroid]3- Zazzagowar bakin mahaifa zuwa kofar farji dalilin haihuwa, wato prolapse (wanda dole sai anje ga likitan Mata wato Gynecologist wannan domin agyara)
4- Infection din cikin mahaifa da sassanta
5- Shigar kwayoyin cuta mafitsara
6- Matsalar basir me tsiro
7- Samuwar ƙari aƙwan halittar Mace [Ovarian cyst]8- Shigar kayan aikin likita jikin Mace yayin magani ko binkicen cuttukan jeji (irinsu; cervical cancer) ko radiyoterafi da kemotirafi.

:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

SAI KUMA DALILAI MASU ALAƘA DA KWAKWALWA

■- Halin fushi; Wato rashin jituwa ta yiwu kila asanda Maigidan yazo ita Matar bataso, kila auren dama babu soyayya ko kuma bakomi sai cusa mata takaici, dama sai yanason jima’i takejin kalamai masu dadi daga garesa… wannan kanyi tasiri ya hana Mace jin dadin komi

■ Gabannin kwanakin haila nan ma normally Mace na iya rika jin zafin jima’i

■- Cutar damuwa ya zamto akwai wani abu ran Macen wato depression, tamkar bayanin sama game da fushi da nayi, wato de ba abama saduwar cikakken attention ba.

■- Yanayin yadda mutum ya bayyana ga Macen wani yakan tsoratata, Musamman idan ka zamto a halitta baka kayatar da ita, inkana da tumbi wato kugunka bai zamto flat ba, inka danneta duk nauyinka baki daya na kan cikinta, kamar zatai amai take ji. Sannan ga karancin tsafta.

■- Idan ya zamto antaɓa cin zarafin Mace wato kamar fyade.

::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

A Maza kuwa sukan fuskanci zafin jima’i amma wajen fitar maniyyi wanda kuma galibi shigar kwayoyin cuta prostate wato chronic prostatitis ke jawo haka,ko infection din mafitsara musamman masu masturbations ko masu Mata fiye da ɗaya ko masu abikan saduwa barkatai, ko Masu dabi’ar saduwa ta dubura.

::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

MATAKAN DA ZA’A ƊAUKA

  1. Idan rashin Ni’ima ne kamar yadda kuke cewa toh asami ruwan dumi adansa gishiri arika zama aciki kamar minti 10 zuwa 20 safe da yamma. Haka zaisa glands din ya bude.
  2. A kuma jiɓanci yawan tsarki da ruwan ɗumi, wanda za’a iya dafawa azuba a flask din shayi a aje duk sanda za’a kama ruwa atsiyaya. Wannan nada kyau koda babu matsalar komi ga mace, kai har namiji na bukatar yawaita tsarki da ruwan ɗumi.
  3. Abune me kyau Mace ta jimanci yin Kegel exercise wato: in tana zaune tana kallo, karatu, ko inta shiga wanka take sa hannu tana damke leɓatun farjinta saita ɗan ja ta riƙe kamar sekons 20 saita saki….taita maimaitawa sekons 20 tana saki tsawon minti 5 zuwa 10, haka za akeyi safe da yamma in ansami dama walau mai aure ko budurwa, is normal. Zai hana toshewar lubricants
  4. Ga Mazaje masu tumbi kuke canza salon kwanciya, ai kokari arage teɓa, kuma kuke kwantawa su Matan suke zamtowa sune samanku.
  5. A tabbatar anyi fitsari kafin jima’i, Sannan arika wanka da ruwan dumi kafin jima’i hakan ma duk na magance matsalar.
  6. Amfani da lubricants wato ruwan da zak sanya a samun santsi da saukakawa wajen shiga wanda ana iya amfani da Man zaitun (olive), K.Y Jelly, Relens, Durex water soluble, LubeLife, ProAdvantage, LoveHoney da sauransu.
  7. A sami fahimtar juna tsakanin Mata da miji, arika cin fruits.
  8. Idan matsalace ta rauni ajikin Macen kamar kuraje, tsagewar farji da sauran infection kamar cervicitis, zubar ruwa me doyi, ko farin ruwa me kauri to ai kokari aje ga likitocin Mata (Gyneacologist) azanta dasu adauki mataki.
  9. Haka Maza masu jin zafi yayin inzali galibi infection ne na prostate lallai sai kunga likita angano abunda ke haddasa hakan anrubuta muku maganin da ya dace.

Allah sa mudace, ya kara mana lafiya tare da zaunar da kasar mu lafiya amin!

✍🏼
[Ibrahim Y. Yusuf]

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button