Fadakarwa

ZAMANTAKEWA

ZAMANTAKEWA: Tunda mijina ya kora ni gida, bai zo ba, bai aiko ba, Ina so in sani ko ya hakura da ni ne ko A’a? – Sakina Lawal a Kotu

Daga Mohammad Lere Kaduna

Wata matan aure Sakina Lawal ta kai karar mijin ta Aliyu Isah kotun Magajin Gari dake Kaduna ta rokon Kotu ta tursasa kotun ya yi mata bayani ko har yanzu yana aurenta ko bayaya yi.

Dalili kuma kamar yadda Sakina ta bayyana wa Alkali a zauren kotu shine ” Tun a watan Oktoba da Mijina Aliyu yakora ni gidan iyaye na bai zo ba sannan bai aiko ba shiru har yanzu bai ce komai ba sannan kuma shi bai ce ya sake ni ba.

” Hakan ya sa na ke so Kotu ta tursasashi ya fadi mini ko yana auren ko ba yayi. Saboda babu wanda ya san inda ya dosa.

Wakilin Aliyu a kotu ya bayyanawa alkali cewa ” Sakina tsigalalliya ce, ga rashin kun sannan. Ba ka isa ka saka ta ba, ba za ka hana ba. Idan ta tashi fita yawon ta sai ta karkada ta yi tafiyarta ban sani ba.

“Dalilin haka ne ya sa da kora ta gida na ce ina zuwa ban je ba. Ina so ta huta a gida a dan yi mata fada tukunna.

  • Aliyu Ya ce yana gyara gidan sa ne yanzu wanda ya ke sa ran nan da sati biyu masu zuwa zai kammala sai ta dawo sannan kuma ya ce zai saka yayan su duka su 6 a makaranta zuwa wannan lokacin.

Alkalin kotun Malam Murtala Nasir ya dage shari’ar zuwa 25 ga watannan, a lokacin ta koma gida sannan Aliyu ya saka Ƴaƴan su a makaranta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button