Videos

Zamu maida chass ta koma yabon Annabi kamar yadda muka maida warr

Zamu maida chass ta koma yabon Annabi kamar yadda muka maida warr

Allah dai ya kara basira babu shakka karin maganar da ake cewa Kano garin masoya Annabi ne wannan magana haka take sannan kuma daman ance Kano tumbin giwa koda me kazo an Fika saboda dukkan wasu abubuwa da ake fada akan Kano yanzu idan ka duba zakaga hakane

Akwai shehin malami wanda zakuna yawon ganinsa acikin Wani film mai suna izzar so yana fadakar da Mutane akan soyayyar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam yace wannan wankar wacce ado gwanja yayi zasu mayar da ita ta yabon Annabi wanda wannan aikin anyi matukar jinjina masa

Waccen ma wakar da ado gwanja yayi anji sun mayar da wakar yabo wanda kuma tayi matukar dadi domin tafi ainihin wakar gwanja ma dadi tunda ita shugaban halitta akayiwa dole ta banbanta da waccen

Shehin malamin yayi wannan ikirarin na cewa zasu juya wakar ta koma wakar yabon annbine saboda yadda suke matukar kanarsa saboda duk duniya bamu da kamarsa shine gatanmu kuma danshi akayimu

An yabawa wannan malamin bisa yadda yake kara zaburar da mutane yadda zasu so shugaban annabawa kuma malamin daman tunda ansa bashi da wani burin wanda ya wuce yaga ana yabon Annabi shi yasa ma yake kokarin juya duk wata waka wacce bata yabon Annabi ba kuma yaga mutane suna jinta sosai sai yayi amfani da wannan damar wajen cusawa mutane kaunar Annabi ta hanyar jin yabonsa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button