ylliX - Online Advertising Network Zan kammala aikin ginin Kurkukun Janguza dake Kano, a Karshen shekarar 2022 - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Zan kammala aikin ginin Kurkukun Janguza dake Kano, a Karshen shekarar 2022

Zan kammala aikin ginin Kurkukun Janguza dake Kano, a Karshen shekarar 2022

Gwamnatin tarayya tasha alwashin kammala aikin ginin Kurkukun Janguza dake Kano, nan da Karshen shekarar 2022 Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin ministan harkokin cikin gida na Najeriya Mista Ra’uf Aregbosola.

 

Ministan ya bada tabbacin ne lokacin ganawarsa da manema labarai a ziyarar da ya kai Kano domin duba yadda aikin ginin sabon gidan gyaran halin na Janguza yake gudana dake yankin karamar hukumar Tofa.

 

 

Acewar Ministan yana da tabbacin cewa, gwamnatin Buhari zata saki kudin da ya kamata a kasafin kudin badi, dan samun damar kammala aikin ginin baki daya.

Ya cigaba da cewa: yaje jihar ne domin ganewa idonsa yadda aikin gina gidan gyaran halin yake tafiya, wanda ya yaba da kokarin ‘yan kwangila da shugabannin dake kula da aikin, bisa yadda suka sanya gaskiya da tsoron Allah a wajen gudanar dashi.

Wakilinmu majiyar mu a rundunonin tsaro, Idris Usman Alhassan, ya rawaito mana cewa: a yayin ziyarar Ministan Ma’aikatar cikin gidan na Najeriya ya yi tattaki a kafa zuwa wasu gine-ginen da aka kammala inda ya nuna gamsuwar sa da aikin.

Daga cikin wadanda suka yiwa Ministan rakiyar duba aikin ginin sabon gidan gyaran halin na Janguza, sun hadarda: Babban Kwantirolan hukumar kula da gidajen ajiya da gyaran hali na kasa Halliru Na Baba da na jihar Kano, Sulaiman Muhammad Inuwa, da kakakin hukumar na kasa dana jihar Kano SC Musbahu Lawal Kofar Nassarawa da Jami’an Hukumomin Civil Deffence da Immigration da kuma Tawagar Ma’aikatarsa da Ministan yazo da ita daga Babban Birnin Taraiya Abuja.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button