Latest Hausa NovelsLABARAI/NEWS

ZANGA-ZANGA: Ɗalibai Mata sunyi barazanar cire dan kamfai saboda yajin aikin ASUU

ZANGA-ZANGA: Ɗalibai Mata sunyi barazanar cire dan kamfai saboda yajin aikin ASUU

Wasu ɗalibai mata na jami’ar ATBU da jami’ar jihar Bauchi da ke Gadau, sun shirya fita tituna zanga-zanga tsirara kan yajin aikin ASUU.

Ɗaya daga cikin matan da suka jagoranci shirya haka ta ce za su yi haka ne domin jawo hankalin FG da ASUU su buɗe makarantu.

Ɗalibai mata sama da 500 daga jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa, da makociyarta Jami’ar jihar Bauchi, Gadau, sun shirya fitowa tituna zanga-zanga a faɗin jihar Bauchi rabin jikinsu tsirara.

Matan sun shirya fara wannan zanga-zanga ne biyo bayan ƙara wa’adin yajin aikin gargaɗi da kungiyar ASUU ta yi, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ɗaya daga cikin ɗalibai matan da suke jagorantar shirya zanga-zangar wacce ta nemi a ɓoye bayananta ta ce:

“A matsayin mu na ɗalibai ma su bin doka, mun jima muna hakuri, goben mu na cikin hatsari saboda wasu tsirarun yan ƙasa da ba abun da ya dame su sai ‘ya’yan su da iyalan su.”

Ta ce zasu bi duk wasu hanyoyin da doka ta tanada wajen matsa wa bangarorin biyu lamba don tabbatar da an buɗe jami’o’in Najeriya nan gaba kaɗan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button