ylliX - Online Advertising Network ZARGIN DAMFARA: Hukumar EFCC Ta Ce Bata San Inda A.A Zaura Ya Shiga Ba - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

ZARGIN DAMFARA: Hukumar EFCC Ta Ce Bata San Inda A.A Zaura Ya Shiga Ba

ZARGIN DAMFARA: Hukumar EFCC Ta Ce Bata San Inda A.A Zaura Ya Shiga Ba

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa EFCC ta ce ba ta san inda ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a jam’iyyar APC, Abdussaalam Abdulkarim (A.A. Zaura), ya shiga ba.

EFCC ta shaida hakan ne a gaban Babbar Kotun Jihar Kano, inda ake zarginsa da hannu wajen damfarar wani ɗan ƙasar Kuwait Dalar Amurka miliyar daya da dubu 300.

An dai shirya dawo da ci gaba da sauraron ƙarar ne a ranar Litinin, bayan Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da umarnin sakinsa tare da sake shari’ar.

Lauyan dan siyasar, Ibrahim Waru, ya ce ba lallai sai wanda yake karewar ya bayyana a gaban kotun ba kasancewar sun shigar da wata ƙarar suna kalubalantar hurumin kotun na sauraron ƙarar.

Kazalika, ya ce wanda yake karewar ba shi da cikakkiyar lafiyar da zai iya tsayawa a gaban kotun, kuma suna da shaidar asibiti a kan hakan Daga bisani kotu ta ɗage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Tun a watan Yunin 2020 ne dai wata kotun ta wanke A.A. Zaura tare da korar ƙarar, lamarin da yasa EFCC ta sake ɗaukaka ƙara domin neman a sake duba shari’ar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button