NEWS

Zazzafan martani da sheike Nura Khalid yayi akan chanzin kudi , ya bayyana hakan a matsayin zalinci

Sheike Nura Khalid babban malami a tarayyar Nigeria ya yi kakkausar suka game da chanzin kudi a Nigeria

 

 

Malamin awani wa’azi daya gabatar ya soki chanzin kudin da za’a yi a tarayyar Nigeria inda ya alakan ta haka da zalinci ƙarara dake kokarin yiwa al umma kasa

 

 

Sheike Nura Khalid dai ya kasance babban malami a tarayyar Nigeria wanda yake sukar ayyukan gomnati musamman idan zasu illata rayuwar talakan kasa

 

 

 

 

Malamai da dama na cigaba da tunatar wa da shugaban kan muhimmancin sanin hakkin al umma da kuma hukuncin takurawa hadi da gallazawa al umma kasa

 

 

 

Wannan na daya daga cikin hudubar da babban malamin masallacin kofar ruwa yayi a juma’a da ta gabata inda ya soki yadda wasu shugabannin suke buris da hakkin da kuma gallazawa talakawa ta hanyoyi da dama

 

 

Malamin ya kara da cewa duk da irin wahala da hukuncin rayuwa da al ummar kasa ke fama da shi harma da rashin tsaro amma hakan bai hana shuwagabannin ɓullo da wata hanyar cutar da al umma ba wato chanzin kudi

 

 

Ba kadai wanna malami ne yayi huduba ba a ranar juma’a,malami da dama duk matukar nuna rashin jin dadin su game da wannan chanzin kudi lamarin da ke cigaba da takurawa al umma tare da gallaza musu

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button