Latest Hausa Novels

ZINA TA GAGARI WANI SAURAYI

ZINA TA GAGARI
WANI SAURAYI👦

Wata rana Wani Saurayi
Yaje wurin wata
Budurwa da niyar
Fasikanci sai yaje ya Gaya mata sai taki Amince wa Sai
ya tafi Sai Bayan ya
qara Dawo wa sai Yace
mata ta Amince Da Abunda yake
buqata tace bazata Amince Ba
yace mata ya Bata duka Dukiyarsa Tace
Bata So
Amma Tana So yayi Abu guda Idan Har
yayi wallahi Zata Amince Sai yace mata
Ta
fadi Komi nene Zaiyi Tace Masa Tana so ya Tsaida Salla kar ya
sake
yayi wasa da ita Har Tsawon Kwana 40 to
Idan Har yai Haka
Wallahi Zata Amince
yace To Shikenan Zai Kwatanta Sai ya tafi da
yaji Anyi Kiran Salla kafin liman ya Shigo
shi
har ya Rigashi Shi
Kullum Haka Yai Tayi
Aka kai kwana 10 aka kai 20 aka kai 30 Ana
cika Rana Ta 40 kawai sai Yarinyar nan
tazo
tace yau ne zata Cika
Mashi Alqawarin Da Ta
Dauka Sai Yace Subahanallai Allah ya Shiryeki to jamaa Cika
Salla akan lokaci tana Hana Alfasha
Kaman Yadda Allah yake Fada a cikin Suratul-Ankabut Aya ta (45) (“Innas-salata Tanha anil fahsha’i Wal-Munkar) zuwa Karshen Aya
Allah yasa Mu Dace ya kuma tsare mu Daga Aikin shedan
Al-barkar Annabi Muhammad (S.A.W.)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button